Isa ga babban shafi
Gambia

Adama Barrow ya karbi rantsuwar kama aiki a Senegal

Sabon shugaban kasar Gambia Adama Barrow ya karbi rantsuwar kama aiki daga Ofishin Jakadancin kasar da ke Senegal.

Adama Barrow ya karbi rantsuwar kama aiki a birnin Dakar na Senegal
Adama Barrow ya karbi rantsuwar kama aiki a birnin Dakar na Senegal SENEGALESE PRESIDENCY / AFP
Talla

An rantsar da Barrow kwananki bayan ya nemi mafaka a birnin Dakar na Senegal, sakamakon turjiya da Yahya Jammeh ya nuna na kin sauka daga mulki bayan shan kaye a zaben watan Jiya.

Rantsar da Barrow mai shekaru 51, a wata kasa ya diga ayar tambaya kan bukatar amfani da karfi wajen komawa birnin Banjul don tafiyar da Mulkin kasar.

Kokarin Kungiyar Ecowas na tursasawa Jammeh sauka daga Mulki bai yi tasiri ba lura da ko-in-kulla da ya nuna, tare da shirye sojin kasar ga duk wani barazana da za a kai wa gwamnatinsa.

A lokacin rantsuwar kama aiki Barrow ya bukaci hadin-kai daga Sojojin kasar da ya bukaci su koma barikinsu.

Mista Barrow ya ce kin biyaya daga Sojin to tamkar sun koma 'yan tawaye ne.

Yanzu dai ana iya cewa Gambia na da shugabanni kasa biyu, guda a cikin kasa guda a wajen kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.