Isa ga babban shafi
Gambia

Babu ranar da Barrow zai koma Gambia

Bayan ficewar tsohon shugaban Gambia Yahya Jammeh daga kasar a ranar Asabar da ta gabata, har yanzu babu wata takamammiyar ranar da zababben shugaban kasar Adama Barrow da ke ci gaba da zama a Senegal zai koma kasar ta Gambia. 

Zababben shugaban Gambia Adama Barrow
Zababben shugaban Gambia Adama Barrow Photo: Seyllou/AFP
Talla

Yanzu haka dai za a iya cewa komawar sabon shugaban na hannun kungiyar kasashen yammacin Afrika, CEDEAO ko kuma ECOWAS.

Manzon Majalisar Dinkin Duniya a yankin, Mohamed Ibn Chambas ya bayyana bukatar ganin  Adama Barrow ya koma gida a cikin gaggawa, in da ya ce bai dace a samu wani tsawon lokaci ba tare da shugaba a Gambia ba.

Lokaci dai na ci gaba da  kwarewa, lura da cewa babu wata rana da aka tsayar a hukumance ta komawar sabon shugaban Adam Barrow.

Manazarta dai na ganin komawar, shugaba Barrow birnin Banjul a cikin gaggawa, shi ne mafi soyuwa.

To amma a cewar Marcel Alain de Souza, shugaban kwamitin gudanarwar Kungiyar Kasashen Yammacin Afrika, Barrow zai koma gida ne bayan an gama tabbatar da matakan tsaro a  birnin na Banjul.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.