Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojoji na gudu su bar mata da ciki a Borno

‘Yan mata da dama ne Sojojin Najeriya suka yi amfani da su kuma kafin matan su gano suna dauke da juna biyu an dauke Sojojin daga Jihar Borno mai fama da rikicin Boko Haram.

Rikicin Boko Haram ya raba mutane sama da miliyan biyu da rabi da gidajensu a arewa maso gabashin Najeriya
Rikicin Boko Haram ya raba mutane sama da miliyan biyu da rabi da gidajensu a arewa maso gabashin Najeriya © Obi Anyadike/IRIN
Talla

Wasu matan da Kamfanin dillacin labaran Faransa AFP ya zanta da su a Maiduguri sun ce sojojin sun jefa rayuwarsu cikin kunci.

Ummi Hassan ‘yar shekaru 18 ta ce tana dauke da ciki watanni biyu aka dauke sojan da ya mata cikin zuwa Lagos kuma ya barta cikin wahala duk da suna magana a waya.

Ummi ta ce abincin da ma za ta ci yana ma ta wahala.

Akwai Kaltime Ari da Amina Muhammed da sojoji suka yi wa ciki kuma har suka haihu ba su yi ido da iyayen ‘ya’yan ba.

Yanzu Matan sun ce sun koma yin bara domin samun na abinci da hidima da ‘yayansu saboda halin kuncin rayuwa da suka tsinci kansu a ciki.

A bara, Kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun zargi sojoji da ‘Yan sanda da ‘Yan kato da gora da yi wa mata fyade a sansanonin 'Yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu.

Kungiyar Human Rights Watch ta ce akwai irin wadannan matsalolin kusan 43 da ta tattara inda jami’an tsaro ke tilastawa mata yin jima’I da su ta hanyar alkawarin za su aure su ko ba su abinci da kudi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.