Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya

Dakarun MDD sun hallaka jagoran 'yan tawaye a Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya

Kungiyar ‘yan tawayen Jamhuriyar Afirka ta tsakiya tace wani harin sama da dakarun Majalisar Dinkin Duniya suka kai garin Bambari ya hallaka wani shugaban ‘yan tawayen da kuma mabiyan sa guda 3.

Daya daga cikin sojojin wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya
Daya daga cikin sojojin wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya
Talla

akakin dakarun samar da zaman lafiyar Majalisar Dinkin Duniya, Vladimir Monteiro ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce sun kai harin ne dan kaucewa barkewar wani sabon tahsin hankali, ganin yadda ‘yan tawayen suka kutsa yankin da ba nasu ba.

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta fada cikin tashin hankali tun bayan kawar da shugaba Francois Bozize daga karagar mulki a shekarar 2013.

Kungiyar ‘yan tawayen FPRC ta jagoranci kawar da Bozize hakan ya haddasa kaddamar da hare haren ramuwa tsakanin Musulmi da Kristoci a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.