Amurka na son a kakabawa Sudan ta Kudu takunkumin sayan makamai
Kasar Amurka ta sake rokon kwamitin Sulhu na Majalisar dinkin Duniya da ya sake nazari kan muhimmanci sanyawa kasar Sudan ta kudu takunkumin sayen makamai saboda yadda al’amura ke ci gaba da tabarbarewa a kasar.
Wallafawa ranar:
Jakadiyar Amurka a kwamitin Nikki Haley tace bukatar Majalisar na tsagaita wuta da baiwa jami’an agaji damar gudanar da ayyukan su da kuma tattaunawa dan warware rikicin kasar sun ci tura.
Zalika Haley ta zargi gwamnatin shugaban Sudan ta Kudun Salva Kiir da kirkirar yunwa a kasar sakamakon gaza aiwatatr da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma da ‘yan tawayen kasar, wanda daga ciki shi ne janye sojin kasar daga tituna zuwa barikokinsu.
Kasashen Faransa da Birtaniya sun goyi bayan matsayin na Amurka amma Rasha da China sun hau kujerar na ki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu