Isa ga babban shafi
Tattalin Arziki

An shigar da haramtattun kudade kasashen Afrika

Wani sakamakon bincike da aka fitar a Amurka ya bayyana cewa haramtattun kudaden da ake shiga da fita da su a kasashen Afrika sun kai kusan dala Tiriliyan 3 da rabi a 2014.

Haramtattun kudaden da ake shiga da fita da su a kasashen Afrika sun kai kusan dala Tiriliyan 3 da  rabi
Haramtattun kudaden da ake shiga da fita da su a kasashen Afrika sun kai kusan dala Tiriliyan 3 da rabi REUTERS/Yves Herman
Talla

Rahoton na zuwa a yayin da ake shirin soma taron tattalin arzikin duniya kan Afrika a birnin Durban na Afrika ta kudu.

Rahoton wanda wata hukumar kula da halattun kudade ta duniya ta gudanar wato GFI ya ce haramtattun kudaden da ake shiga da fita da su a kasashe masu tasowa sun kai tsakanin dala Triliyan 2 zuwa 3 da rabi a shekarar 2014.

Kuma rahoton ya ce matsalar ta fi shafar Afrika da ake shigowa da fitar da kudaden domin bukatu da suka shafi saka jari.

Binciken yace adadin haramtattun kudaden da ake shige da fice da su sun kai kusan kashi 24 na kasuwancin kasashen masu tasowa tsakanin 2005 zuwa 2014, shekarar karshe da aka tattara sakamakon binciken.

Sai dai masharhanta a fannin ci gaba sun ce yawanci kasashen kudu da Sahara na dogaro ne da tallafi daga manyan kasashe wadanda kuma ke kasancewa kudaden jari ga wasu.

Rahoton ya zargi Rasha da wasu kasashen gabashin Turai na tsohuwar daular soviet a matsayin inda aka fi shige da ficen kudaden na kasuwancin yankin.

Matsalar dai na haifar da salwantar kudaden wata kasa musamman idan sun bar kasar ba za su sake dawo wa kasar da ke da mallakinsu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.