Isa ga babban shafi
COTE D'IVOIRE

Gwamnatin Cote D'Ivoire na kokarin shawo kan tsoffin 'yan tawaye

Sojojin Gwamnatin kasar Cote d’Ivoire na ci gaba da kutsa kai birnin Bouake dan murkushe tsoffin ‘yan Tawayen dake bore tareda haifar da tashin hankali saboda rashin biyan su kudaden alawus.

Tsoffin  'yan tawaye masu bore  a Cote D'Ivoire
Tsoffin 'yan tawaye masu bore a Cote D'Ivoire REUTERS/Luc Gnago
Talla

Shugaban rundunar sojin kasar , Janar Sekou Toure ya bayyana boren tsoffin Yan Tawayen a matsayin abinda ya karya ka’ida, saboda haka ya baiwa dakarun su umurnin tabbatar da doka da oda a biranen Bouake da Abidjan.

Kafin dai wannan umurni, gwamnatin Cote d’Ivoire na ci gaba da kaucewa daukar matakan soji kan boren Yan Tawayen.

Kakakin Yan tawayen, Seydou Kone yace sun gana da sojojin a Tiebissou, inda suka basu umurnin aje makaman su, amma suka ki cewa dole sai an biya su.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.