Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

‘‘Akwai yiwuwar raba Zuma da kujerarsa’’

Sakatare Janar na Jam’iyyar ANC a kasar Afirka ta kudu, Gwede Mantashe, ya ce akwai alamun cewar ana iya raba shugaba Jacob Zuma da mukamin sa bayan babban taron Jam’iyyar da za’ayi a wata Disamba mai zuwa.

Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma na Fuskantar matsalar a Jam'iyyarsa ta ANC
Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma na Fuskantar matsalar a Jam'iyyarsa ta ANC REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Bisa ka’ida a taron jam’iyyar ne za’a zabi sabon shugaban da zai jagorance ta, kafin shekarar 2019 a gudanar da zaben shugaban kasa.

Sai dai rahotanni na nuna cewar wasu daga cikin manyan 'Yan Jam’iyyar zasu tilastawa shugaban mara farin jinni ya sauka daga mukaminsa.

Mantashe ya yi misali da shugaba Thabo Mbeki wanda shima ya sauka daga shugabancin kasar bayan ya rasa mukamin shugaban Jam’iyyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.