Wade zai koma Senegal don yakin neman zabe
A yayin da ake shirin soma yakin neman zabe a Senegal a gobe Lahadi, tsohon shugaban kasar Abdoulaye Wade ya sanar cewa yana kan hanyarsa zuwa Dakar a ranar Litinin domin yakin neman zabe.
Wallafawa ranar:
Tsohon shugaban ya shaidawa wata kafar yada labaran talabijin ta Senegal cewa zai dawo domin shiga siyasa gadan gadan inda shi ne yanzu shugaban jam’iyyar gungun ‘yan adawa ta Wattu Senegal
Sannan ya tabbatar da goyon bayansa ga dansa Karim Wade da zai tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2019.
A ranar 30 ga watan Yuli ne za a gudanar da zaben Yan majalisu a Senegal, kuma wasu na ganin dawowar Wade barazana ne ga shugaba Macky Sall da sauran jam’iyyun da ke kawance da gwamnatinsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu