Isa ga babban shafi
Congo

Da wahala a yi zaben Jamhuriyyar Congo a bana

Shugabar Hukumar zaben Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo Corneille Nangaa’a ta ce yana da matukar wuya kasar ta gudanar da zaben shugaban kasa a wannan shekara, matakin da ake ganin zai sabawa yarjejeniyar da bangarorin siyasar suka taka.

Dage zaben kafin watan Disemba zai ba Joseph Kabila damar ci gaba da shugabanci
Dage zaben kafin watan Disemba zai ba Joseph Kabila damar ci gaba da shugabanci REUTERS/Yves Herman/File Photo
Talla

Jami’ar ta shaidawa manema labarai cewar a halin da suke ciki yanzu haka babu yadda za su iya gudanar da zaben a watan Disamba mai zuwa.

A karkashin yarjejeniyar da bangarorin siyasar kasar suka amince da ita bara, yarjejeniyar ta haramtawa shugaba Joseph Kabila sake takara.

Shugaban ‘yan adawar kasar, Felix Tshikesedi ya ce za su mayar da martanin da ya dace nan gaba kadan.

Shugaban hukumar zaben ta bayar dalilai na tsaro musamman rikici a yankin Kasai da za su sa a dage lokacin zaben da aka amince kafin Disemba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.