Isa ga babban shafi
Angola-Tarayyar Turai

Angola ta yi watsi da bukatar Tarayyar Turai

Angola ta ki amincewa da bukatun tawagar masu sa ido na kungiyar Tarayyar Turai dangane da neman halartar kasancewar su a zaben kasar mai zuwa.Tawagar dai ta bukaci da a ba ta damar sanya wakilci a runfunan kasar yayin babban zabe mai zuwa da za a gudanar ranar 23 ga watan Agusta.

shugaban Angola José Eduardo dos Santos
shugaban Angola José Eduardo dos Santos REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Ministan harkokin wajen kasar Georges Chicoti ya sanar da cewa ba sa bukatar tsoma bakin wasu a harkokin zaben kasar ta hanyar fakewa da sanya idanu.

A cewar ministan, Angola nahiyar Afrika ce, don haka kungiyoyin da suka amince su tsoma baki a harkokin zabensu ba za su wuce na Tarayyar Afrika da kuma na yammacin Afrika ba.

George Chicoti ya ce matakan tsaro su ne abin dubawa idan aka ce an amincewa da kasancewar masu sanya ido na Turai a dukkanin yankunan kasar 18.

Sai dai a cewar kakakin Tarayyan Turan Pablo Mazarrasa har yanzu kungiyar ba ta kai ga cimma matsayar turo jami'an sanya idanun ga zaben kasar Angolan ba.

Tun a shekarar 1979 ne dai shugaba Eduardo Jose Dos Santos ke shugabancin kasar ta Angola, kuma rashin tsayawar sa a takarar zaben na watan Augusta me zuwa ana ganin zai iya samar da sauyi a harkokin gudanarwar kasar.

Duk da kasancewar Angola guda cikin manyan kasashen da ke fitar da mai a kasashen saharar Afrika amma har yanzu al'ummar kasar na fama da matsanancin talauci idan aka kwatanta da takwarorinsu na nahiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.