Isa ga babban shafi
Rwanda

Shugaba Paul Kagame ya karbi rantsuwar soma aiki a yau

An rantsar da shugaban kasar Rwanda Paul Kagame wa’adi na uku sakamakon nasarar zaben da ya samu na kusan kashi 99 na kuri’un da aka kada. Shugabannin kasashe 19 suka halarci bikin wanda aka gudanar a gaban dubban mutane a Kigali.

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame
Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame Paul Kagame Twitter
Talla

Kagame yayi shagube ga masu sukar yadda aka gudanar da zaben, inda yake cewa babu wata kasa da zata tilasta musu bin tafarkin ta wajen gudanar da mulki.

Shugaban yace ba zasu amince da bin siyasar kasashen duniya ba wanda suma al’ummar kasar su sun gaji da ita.

Shugaba Kagame da ya fara jagorantar Rwanda tun bayan kawo karshen kisan kare dangi a shekarar 1994, ya samu sama da kashi 98 cikin 100 na kuri’un da aka kada.

Sai dai ana zargin shugaban da yin mulkin kama-karya, amma mutanen kasar na yaba ma sa saboda rawar da ya taka wajen inganta tattalin arzikinsu.

Kimanin mutane miliyan 6 da dubu 900 ne suka fito don kada kuri’unsu, yayin da Kagame mai shekaru 59 ya shafe tsawon shekaru 17 akan karagar mulki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.