Kotun kolin Kenya ta soke zaben shugabancin kasar
Kotun Kolin Kenya ta soke zaben shugabancin kasar da aka gudanar a watan jiya, in da aka ayyana Uhuru Kenyatta a matsayin wanda ya yi nasara.
Wallafawa ranar:
A cewar Kotun ta dauki matakin ne sakamakon kura-kuren da aka samu a zaben, yayin da ta bada umarknin sake gudanar da wani zaben cikin kwanaki 60.
Sai dai shugaba Uhuru Kenyatta ya ki amince wa da hukucin kotun, amma duk da haka zai mutunta umarninta kamar yadda ya shaida wa manema labarai.
Shi kuwa babba abokin hamayyar Kenyatta, wato Raila Odinga ya yaba da matakin Kotun, wanda y ace, shi ne irinsa na farko a nahiyar Afrika.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu