Isa ga babban shafi
Togo

'Yan adawa a Togo sun jajirce kan bukatar sauya tsarin mulkin kasar

Shugabanin adawa a Togo sun ce, ba abin da su ke bukata face sauya kundin tsarin mulkin kasar, sabanin sauye sauyen da gwamnati ta yi alkawarin samarwa. Hakan dai na zuwa ne bayan zanga zangar kin jinin gwamnatin da 'yan adawar suka rika gudanarwa a baya-bayan nan, wadda ta samu halartar dubban yan adawa a manyan biranen kasar.

Yau shekaru 10 ke nan  yan adawar ta Togo ke bukatar ganin an sake fasalta kundin tsarin mulkin 2002 da aka kwaskwarimance, musaman ta bagaren sake maido da dokar takaita waádin shugabancin kasa  shekaru 10 a waádin shekaru biyar biyar sau 2 babu kari.
Yau shekaru 10 ke nan yan adawar ta Togo ke bukatar ganin an sake fasalta kundin tsarin mulkin 2002 da aka kwaskwarimance, musaman ta bagaren sake maido da dokar takaita waádin shugabancin kasa shekaru 10 a waádin shekaru biyar biyar sau 2 babu kari. Reuters
Talla

Eric Dupuy, kakakin hadakar jamíyyun adawar 5 Cap 2015 – kungiyar da ta jagoranci zanga zangar ranakun laraba da Alhamis, domin ganin a siyasance an samar da sauyin gwamnati a Togo, ya danganta sauye sauyen da gwamnatin ta ce za ta samar a matsayin jan kafa, inda yace ba shi ne abinda su ke bukata ba.

Shugaban kasar ta Togo, Faure Gnassingbé, ya dare kan karagar shugabancin kasar shekaru 12 da suka gabata bayan mutuwar mahaifinsa, Gnassingbé Eyadéma.

Mahaifinsa janar Eyadéma ya mulki yar karamar kasar ta Togo da ke yankin yammacin nahiyar Afrika na tsawon shekaru 40 sakamakon wani juyin mulkin soja da ya yi wa gwamnatin farar hula.

Yau shekaru 10 ke nan yan adawar ta Togo ke bukatar ganin an sake fasalta kundin tsarin mulkin 2002 da aka kwaskwarimance, musaman ta bagaren sake mai do da dokar takaita waádin shugabancin kasa shekaru 10 a waádin shekaru biyar biyar sau 2 babu kari.

A wata sanarwar bayan taron majalisar ministoci ta marecen ranar talatar da ta gabata , gwamnati ta yi wani yinkuri da ake ganin sassauci ne akan matsayinta, inda ta bayyana aniyar samar da gyare gyare ga kundin tsarin mulkin musaman ta bangaren takaita waádin shugabanci da kuma tsarin zabe da ke kunshe a kundin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.