An fara makokin kwanaki 3 a Somalia
Gwamnatin Somaliya ta sanar da makokin kwanaki 3 bayan tagwayen hare-haren kunar bakin waken da aka kai birnin Mogadishu a jiya da ya hallaka akalla mutane 137.
Wallafawa ranar:
A cewar shugaba Muhammad Abdullahi Muhammad Farmaajo za a fara makokin daga yau Lahadi don nuna alhini ga mutanen da suka rasa rayukansu.
Kawo yanzu akwai sama da mutane 250 da ke karbar kulawar gaggawa a asibitoci bayan samun munanan raunuka sanadiyyar harin na jiya.
Wannan dai shi ne mafi munin hari da aka kai birnin na Mogadishu cikin shekarun nan, inda a bangare guda kuma shugaba Muhammad ya bukaci al’umma su tallafawa mutanen da harin ya rutsa da su.
Har ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta yi ikirarin kai harin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu