Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Mnangagwa na shan suka a Zimbabwe

Sabon shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa na shan caccaka bayan ya nada manyan sojojin kasar a cikin Majalisar Ministocinsa, in da ya ba su manyan mukamai.

Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa
Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Nadin ya nuna cewa, Janar Sibusiso Moyo da ya jagoranci sanar da karbe mulki daga hannun Robert Mugabe ta kafar talabijin a watan jiya, zai rike mukamin Ministan Harkokin Waje, yayin da wasu ke cewa ba shi da kwarewar kula da wannan bangaren.

Sabon shugaban ya kuma nada Perence Shiri da ya shafe tsawon lokaci ya na jagorantar rundunar sojin saman kasar a matsayin Ministan Filaye da ayyukan gona.

Mukamin Perence na da matukar muhimmanci a kasar, lura da takardamar da ake yi kan filayen da aka kwace daga hannun manoma fararen fata kusan shekaru 20 da suka gabata.

Tuni masu sanya ido a siyasar kasar da sauran al’ummar Zimbabwe suka caccaki nadin Mnangagwa.

Sai dai gwamnatin kasar ta kare kanta, in da ta ce, ta nada sojojin ne don tabbatar da adalci a nadin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.