Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Ranar haihuwar Mugabe ta zama ranar hutu a Zimbabwe

Kasar Zimbabwe na cigaba da daukan matakan karrama tsohon shugaban kasar da aka sauke Robert Mugabe, inda a baya-bayan nan ta mayar da ranar tunawa da haihuwarsa na kowace shekara ta zamo ranar hutu.

Tsohon shugaban na Zimbabwe na ci gaba da samun karramawa tun bayan sanar da Murabus din sa a makon daya gabata.
Tsohon shugaban na Zimbabwe na ci gaba da samun karramawa tun bayan sanar da Murabus din sa a makon daya gabata. REUTERS/Mike Hutchings/File Photo
Talla

Matakin na zuwa ne bayan da bangaren matasan jam’iyyar ZANU-PF mai mulki ya roki hukumomin kasar da su amince, inda kuma gwamnatin kasar ta amince da cewa daga yanzu duk ranar 21 ga watan Fabrairun kowace shekara za ta rika zama ranar hutu, wadda za a kira ta da ranar matasa don tunawa da Robert Mugabe.

Ko a makon da ya gabata ma dai kasar ta amince da rada wa filin saukar jiragen sama mafi girma na kasar sunan tsohon shugaban kasar wanda ya kwashe kusan shekaru 40 yana mulkin kasar.

Daga cikin saurarn wuraren da aka rada ma sunan tsohon shugaban kasar har da kwalejin nazarin bayanan sirri ta kasar, yayin da ake kan aikin gina wata jami’a wacce ita ma za a rada mata sunan shugaba Mugabe.

Yanzu haka dai hanyoyi da kuma gine-gine da dama ne a kasar ta Zimbabwe aka riga aka nada masu sunan tsohon shugaban kasar.

Mugabe dais hi ne tsohon shugaban kasar da aka maye gurbin shi da tsohon mataimakin sa, Emmanuel Manangagwa, bayan da sojoji suka hambarar da shi, a lokacin da ya yi kokarin kakaba uwargidansa kan mukaminmataimakin shugabar kasa, domin share mata hanyar da za ta gaje shi bayan ya sauka daga mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.