Isa ga babban shafi

MDD ta kwashe sama 'yan gudun hijira 1, 000 daga Libya

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR, ta ce daga watan Nuwamban bara zuwa yanzu, ta kwashe ‘yan gudun hijira dubu 1,084 daga kasar Libya.

Wasu daga cikin 'yan gudun hijira da Majalisar Dinkin Duniya ta kwashe daga Tripoli, yayin da suka sauka filin jiragen sama na sojin Italiya da ke birnin Rome. 22 ga Disamba, 2017.
Wasu daga cikin 'yan gudun hijira da Majalisar Dinkin Duniya ta kwashe daga Tripoli, yayin da suka sauka filin jiragen sama na sojin Italiya da ke birnin Rome. 22 ga Disamba, 2017. REUTERS/Alessandro Bianchi
Talla

Jakadan hukumar kula da ‘yan gudun hijirar Vincent Cochetel wanda ya bayyana haka a birnin Washington, ya ce a ranar Talata da ta gabata, aka kwashe ‘yan gudun hijira 128 daga Libya zuwa birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar.

Cochetel ya kara da cewa a ranar Laraba jirgi na biyu ya kwashe ‘yan gudun hijira 150 daga birnin Tripoli zuwa babban birnin kasar Italiya Rome, hakan yasa alkalumman ‘yan gudun hijirar da aka kwashe daga Libya ya haura dubu daya, watanni uku bayan kaddamar da shirin kwashe su daga kasar da Majalisar Dinkin Duniya ta yi.

‘Yan gudun hijira daga Afrika sun dade suna bi ta cikin Libya domin ketarawa zuwa kudancin nahiyar Turai, sai dai bayan gano irin azabar da ake ganawa da dama daga cikinsu a wasu sansanoni tsare bakin haure da aka kafa a Libyan, kasashen duniya suka sha alwashin kawo karshen matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.