Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotu ta sallami 'yan boko haram 475

Wata babbar kotu a Najeriya da ke shari’ar mayakan Boko Haram a Kainji jihar Naija, ta sallami wasu mutane 475 da a ke zargi da alaka da kungiyar domin bada damar sauya musu dabi’u.

Wasu mayakan Boko haram da suka mika kai suna tare da sojojin kasar Chadi
Wasu mayakan Boko haram da suka mika kai suna tare da sojojin kasar Chadi REUTERS/Moumine Ngarmbassa
Talla

A farkon makon da ya gabata ne babbar kotun da ke Kainji a jihar Naija, ta fara sauraron shari’ar daruruwan mutanen da aka kama, bisa alakarsu da kungiyar Boko Haram, wadda ke cigaba da gudana.

Ma’aikatar shara’ar Najeriya tace babban dalilin da ya sa kotu ta sallami wadanda ake zargi, shi ne rashin kwararan hujjoji ko shaida.

Jimillar mutane 475 din da kotu ta saki sun kunshi wadanda ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne ko kuma sun boye bayanan da zasu taimakawa hukumomin tsaro wajen dakile hare-haren mayakan kungiyar.

Mutum na farko da kotun ta yankewa hukunci shi ne, dan kungiyar da ya jagoranci sace ‘yan makarantar Sakandaren Chibok a shekarar 2014, wanda ta yankewa hukuncin zaman gidan yari na shekaru 15.

A watan Oktoban shekarar bara, ma’aikatar shari’ar Najeriya ta sanar da yankewa ‘yan kungiyar Boko Haram 45 hukunci. Yayin da aka saki wasu da ake zargin suna da alaka da kungiyar 468, wasu 28 kuma aka ci gaba da tsare su a Abuja da Minna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.