Sama da 'yan Jamhuriyar Congo 57,000 sun tsere zuwa Uganda
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce sama da ‘yan kasar Jamhuriyar Congo 57,000 sun tsere zuwa makwabciyar su Uganda a cikin wannan shekara.
Wallafawa ranar:
Hukumar ta ce adadi ya zarta na shekarar bara ta 2017, inda ‘yan kasar sama da 44,000 suka tsere zuwa Ugandar.
Dubban ‘yan kasar ta Jamhuriyar Congo na gujewa rikicin kabilanci ne musamman inda ya yi kamari a lardin Ituri da ke arewa maso gabashin kasar.
Ana gwabza kazamin rikicin ne tsakanin manoma na kabilar Lendu da kuma makiyaya na kabilar Hema akan mallakar filaye, kuma zuwa yanzu an hallaka mutane 130 daga dukkanin bangarorin, tun bayan sake tashin rikici tsakaninsu a watan Disambar bara, lamarin da ya raba mutane 20,000 da muhallansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu