Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo

Sojin Jamhuriyar Congo sun hallaka 'yan tawaye 13

Rundunar sojin Jamhuriyar Congo, ta sanar da hallaka wasu mayakan ‘yan tawaye 13 yayin fafatawar da suka yi da kungiyar mayakan da basu tantance ba a lardin Ituri da ke arewa maso gabashin kasar.

Jami'an sojin Jamhuriyar Congo.
Jami'an sojin Jamhuriyar Congo. Reuters
Talla

Kakakin sojojin na Jamhuriyar Congo, Jules Ngongo ya ce jami’insu daya ya hallaka, yayinda mayakan suka jikkata wasu guda 2.

Lardin Ituri, shi ne yanki na baya bayan nan a Jamhuriyar Congo da ya fada cikin kazamin rikici na siyasa da kuma fuskantar hare-haren ‘yan tawaye, tun bayanda shugaban kasar Joseph Kabila, ya ki amincewa ya sauka daga mulki, bayan karewar wa’adinsa a Disamba na shekarar 2016.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.