Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo

Jamhuriyar Congo ta zargi MDD da bata mata suna

Gwamnatin Jamhuriyar Congo ta ce ba zata halarci taron kafawa kasar gidauniyar kudaden taimako ba, wanda zai gudana wata mai kamawa a birnin Geneva.

Shugaban Jamhuriyar Congo Joseph Kabila.
Shugaban Jamhuriyar Congo Joseph Kabila. REUTERS/Kenny Katombe
Talla

Taron kafa gidauniyar, na sa ran samun taimakon dala biliyan don agazawa miliyoyin ‘yan kasar.

Mukaddashin Fira Ministan kasar Jose makila ya ce gwamnati ta dauki matakin ne saboda bata mata suna da majalisar dinkin duniya ta ke a idon duniya, dalilin da ya sanya masu zuba hannun jari kauracewa kasar.

Makila ya zargi majalisar da wuce gona da iri wajen kara girmama masifar da ‘yan kasar ke ciki, bayan matakin halin da suke ciki bai kai haka ba.

Majalisar dinkin duniya ta ce sama da ‘yan Jamhuriyar Congo miliyan 13 ke bukatar agajin gaggawa, yayin da kusan ‘yan kasar miliyan 5 suka rasa muhallansu sakamakon tashin hankali.

Jamhuriyar Congo na daga cikin kasashen duniya masu dimbin arzikin ma’adanai daban daban, sai dai har yanzu ‘yan kasar sun gaza amfana da arzikin, sakamakon fama da rikice rikicen kabilanci da na kungiyoyin ‘yan tawaye, sai kuma rikicin siyasar kasar da ke dada zafafa da cin hanci da Rashawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.