Isa ga babban shafi
Libya

Sojin Haftar sun farmaki 'yan tawayen Chadi a gabashin Libya

Dakarun sojin da ke biyayya ga Janar Haftar daya daga cikin shugabanin da ke rike da wasu yankuna a kasar Libya sun kai farmaki kan 'yan tawayen Chadi da ke da maboya a yankin gabashin kasar ta Libya.Rahotanni sun ce dakarun na Haftar sun yi amfani da wasu nau'ikan jiragen yaki wajen kai farmakin da ya kai ga hallaka tarin 'yan tawayen. 

Kungiyar 'Yan tawayen na Chadi wadda ke barazana ga tsaron Libya ta kafu ne tun a shekarar 1960.
Kungiyar 'Yan tawayen na Chadi wadda ke barazana ga tsaron Libya ta kafu ne tun a shekarar 1960. CELLOU BINANI / AFP
Talla

Wasu jiragen yakin dakarun na Janar Khalifa Haftar sun yi luguden wuta kan 'yan tawayen na Chadi da ke kan iyakar kasar da Libya, matakin da ke da nufin dinke barakar da ke tsakanin kasashen biyu tun bayan mutuwar Shugaba Mu'ammar Gaddafi.

'Yan tawayen wadanda yanzu haka su ke rike da ikon wani yanki na gabashin Libyan tun bayan rikicin da ya tagayyara kasar, kuma suna taka muhimmiyar rawa wajen kawo cikas a harkokin tsaron kasashen biyu.

Janar Khalifa Haftar wanda ke jagorancin wani bangare na kasar ta Libya na kokarin ganin ya shawo kan dai dai kun kungiyoyi a kasar don samun goyan baya da nufin wanzar da zaman lafiya a kasar wadda ke fama da rikici tun bayan boren yunkurin kifare da gwamnatin shugaba Mu'ammar Gaddafi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.