Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo

Za a gudanar da taron tallafawa yan gudun hijirar Congo a Geneva

Shugaban jamhuriyar Demokuradiyyar Congo Joseph Kabila ya gana da babban jami’in hukumar yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya Fillipo Grandi a Kinshasha.

Joseph Kabila,Shugaban Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo
Joseph Kabila,Shugaban Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo Thomas NICOLON / AFP
Talla

Babban jami’in ya samu isowa kasar ne da nufin shawo kan hukumomin Kinshasha don gani sun bayar da hadin kai zuwa shirya babban taron samarwa yan gudun hijira da yaki ya tilastawa barin gidajen su tallafin a babban taron Geneva da zai gudana ranar 13 ga wannan watan Afrilu.

Fillipo Grandi bayan ganawa da Shugaban kasar Joseph Kabila ya sheidawa manema labarai cewa ya na da yakinin hukumomin kasar za su kasance a wannan babban taro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.