Isa ga babban shafi
Jamhuriyar demokradiyyar Congo

'Yan adawar Jamhuriyar Congo sun gaza cimma matsaya da Kabila

‘Yan darikar Katolika tare da hadin gwiwar 'Yan adawa a Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo sun gaza cimma yarjejeniyar tsakaninsu da gwamnatin Kinshasa dangane da zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a ranakun Lahadi da litinin don ci gaba da matsa lamba tare da nuna adawa ga shugaba Jopseph Kabila da ya ki sauka daga mulki bayan karewar wa'adinsa.

Tun kafin yanzu dai kungiyoyin kare hakkin dan Adam na duniya dama Majalisar dinkin Duniya sun bukaci Shugaba Joseph Kabila ya mutunta yarjejeniyar 2016 tare da amsa bukatar al'ummar kasar don sauka daga karagal mulki.
Tun kafin yanzu dai kungiyoyin kare hakkin dan Adam na duniya dama Majalisar dinkin Duniya sun bukaci Shugaba Joseph Kabila ya mutunta yarjejeniyar 2016 tare da amsa bukatar al'ummar kasar don sauka daga karagal mulki. REUTERS/Kenny Katombe
Talla

Bangarorin biyu na ‘yan adawar da kuma mabiya Katolika sun ce ba su cimma matsaya a tattaunawar da suka yi da Gwamnan Kinshasa ba, a kokarin da suke na ci gaba da zanga-zangar a gobe Lahadi da kuma jibi Litinin.

Bangarorin biyu dai na bukatar Shugaba Joseph Kabila ya sauka daga mulki tare da gudanar da sahihin zabe a kasar mai fama da rikicin siyasa.

Sai dai bayan sanarwar Bangarorin biyu na gaza cimma yarjejeniya game da zanga-zangar ta gobe, kawo yanzu daruruwan magoya bayan gwamnati suka mamaye babbar majami'ar Katolika da ke birnin na Kinshasa don nuna adawarsu da matakin.

Ko a watan da ya gabata ma makamanciyar zanga-zangar ta haddasa mutuwar akalla ‘yan adawa 15 da ake zargin jami’an tsaron kasar da harbewa ko da yake dai gwamnatin kasar ta ce mutum biyu ne kadai suka mutu.

Shugaban kasar Joseph Kabila wanda wa'adinsa ya kammala karewa amma ya yi kememe ya ki sauka daga mulki, ya sanya dokar haramta duk wata zanga-zangar adawa da mulkinsa a fadin kasar, yayin da dokar ta fi tsananta a Kinshasa babban birnin kasar.

Shugaba Kabila da ya gaji mulki daga mahaifinsa da aka kashe a shekarar 2001, Laurent Kabila na ci gaba da nuna turjiyar sauka daga mulki inda ya ce sai a karshen 2018 za a gudanar da wani sabon zaben kasar.

Tun kafin yanzu dai kungiyoyin kare hakkin dan Adam na duniya dama Majalisar dinkin Duniya sun bukaci Shugaba Joseph Kabila ya mutunta yarjejeniyar 2016 tare da amsa bukatar al'ummar kasar don sauka daga karagal mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.