Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo

Kabila ya yi watsi da zargin take hakkin dan adam

Shugaban kasar Jamhuriyar Congo Joseph Kabila ya yi watsi da zarge-zargen da ake yi wa gwamnatinsa, na amfani da jami’an tsaro wajen cin zarafin ‘yan kasar da ke zanga-zangar neman ya yi murabus, inda ya zargi masu zanga zangar da kai wa jami’an tsaron hari.

Shugaban Jamhuriyyar Dimokaradiyyar Congo Joseph Kabila.
Shugaban Jamhuriyyar Dimokaradiyyar Congo Joseph Kabila. REUTERS/Kenny Katombe
Talla

Karo na farko kenan da Kabila ya gabatar da jawabi ga manema labarai cikin shekaru 6, bayanda a makon jiya, ‘yan sanda kasar suka buge wuta kan malaman Coci mabiya darikar katolika a birnin Kinshasa, yayin da suke zanga-zangar neman ya sauka daga mulki.

Sai da fa shugaban Jamhuriyar Congon ya ki cewa komai, dangane da tsayar da lokacin gudanar da zaben shugaban kasa, wanda kuma shi ne dalilin da ya ke ci gaba da haddasa tarzoma da zanga-zanga a sassan kasar.

‘yan kasar Jamhuriyar Congo masu yawan gaske ne suka rasa rayukansu cikin shekarar 2017 da ta gabata, yayin da suke zanga-zangar tilastawa Joseph Kabila ya yi murabus.

Shugabannin Kiristoci na darikar katolika da ke kasar ne suka shirya gudanar jerin zanga-zangar, sakamakon kin amincewar Kabila ya sauka daga shugabanci, bayan karewar wa’adinsa a watan Disambar 2016, tare da jinkirta gudanar da sabon zabe.

Tun a shekarar 2001 Joseph Kabila ya dare shugabancin Jamhuriyar Congo, bayan hallaka mahaifinsa, tsohon shugaban kasa da aka yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.