Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojin Najeriya sun farmaki maboyar Boko Haram a Borno

Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da kai farmaki wata maboyar mayakan Boko Haram da ke kauyen Arege da Tumbin Rago a jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin kasar.

Rundunar Sojin Najeriyar ta ce bazata kakkauta da kai hare-hare kan mayakan Boko Haram ba har sai ta tabbatar da kakkabe su baki daya.
Rundunar Sojin Najeriyar ta ce bazata kakkauta da kai hare-hare kan mayakan Boko Haram ba har sai ta tabbatar da kakkabe su baki daya. STEFAN HEUNIS / AFP
Talla

Wata sanarwar Rundunar Sojin saman Najeriyar mai dauke da sa hannun kakakinta Air vice Marshal Olatokunbo Adesanya ta ce dakarunta da ke cikin Rundunar Operation Lafiya Dole sun hallaka da dama daga cikin mayakan baya ga kwace makamai da kuma lalata ababen hawansu.

A baya-bayan nan Rundunar Sojin Najeriyar na ci gaba da kai farmaki ba kakkautawa kan mayakan na Boko Haram, inda ko a cikin makon da ya gabata sai da suka tseretar da daruruwan fararen hula.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.