Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari zai dawo Najeriya a yammacin yau

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na kan hanyar sa ta dawowa gida a yammacin yau Alhamis bayan ziyarar da ya kai Kasar Amurka bisa gayyatar shugaban kasar Donald Trump.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. NAN
Talla

Mai magana da yawun shugaban Najeriyar Mr Femi Adesina ya ce a yammacin yau ne Muhammadu Buhari zai iso Najeriya bayan wani tsaiko da jirginsa ya fuskanta wanda ya tilasta masa tsayawa a Birnin London na kasar Birtaniya.

Sanarwar ta Mr Femi Adesina ta kawo karshen tantamar da ake da ita kan abin da ya tsayar da shugaban a birnin London kwanaki biyu bayan barowarshi Amurka ranar Talata.

A safiyar yau ne dai mataimakin shugaban Najeriyar na musamman kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya ce wani tsaiko ne ya tsayar da shugaban a birnin London.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.