Isa ga babban shafi
Kamaru-Amurka

Kamaru ta caccaki Amurka kan zargin sojinta da kisan 'yan aware

Gwamnatin Kamaru ta cacaki kasar Amurka kan zargin da ta yi wa sojojinta na kashe fararen hular da ba su ji ba su gani ba, a Yankin da ake samu tashin hankalin Yan aware masu amfani da Turancin Ingilishi.

Wasu jami'an sojin Kamaru kenan lokacin da su ke sintiri a yankin 'yan aware masu amfani da turancin Ingilishi da ke fama da rikici.
Wasu jami'an sojin Kamaru kenan lokacin da su ke sintiri a yankin 'yan aware masu amfani da turancin Ingilishi da ke fama da rikici. REUTERS/Joe Penney
Talla

Gwamnatin Kasar Kamaru ta hannun ma’aikatar harkokin wajenta ta bayyana bacin ran ta ga Jakadan Amurka Peter Barlerin saboda kalaman sa wanda ya zargi sojojin kasar da kashe fararen hular da ba su ji ba su gani ba a Yankin Yan aware da ke amfani da Turancin Ingilishi.

Jakadan Amurka ya ce matakin da sojojin na Kamaru ke dauka na amfani da karfin da ya wuce kima ya saba ka'ida, yayin da ya zargi Yan aware suma da kashe jami’an tsaro da garkuwa da mutane da kuma kona makarantu.

Wadannan kamalami dai ba su yi wa gwamnatin Kamaru dadi ba, abinda ya sa ta aike da sammaci ga Jakadan domin yi mata bayani akai.

Ma’aikatar harkokin wajen ta ce duk da hare hare da kisan da Yan awaren ke yi, Jami’an tsaron Kamaru na gudanar da ayyukan su kamar yadad doka ta tanada.

Ofishin jinkai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce akalla mutane 160,000 suka zama yan gudun hijira sakamakon rikicin, yayin da sama da 20,000 suka samu mafaka a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.