Isa ga babban shafi
Kamaru

An tube jagoran ayyukan Soji a yankin 'yan awaren kamaru

A kasar Kamaru an tube janar Donatien Nouma Melingui da ke jagorantar ayyukan soji a yankin da ke amfani da Turanci Ingilishi daga mukaminsa. Tube janar Melingui na zuwa a dai dai lokacin da tashe-tashen hankula ke kara ta'azzara a yankin mai amfani da turancin Ingilishi.

Matakin dai na tabbatar da zargin da ake yiwa dakarun sojin da aiwatar da kisan kiyashi kan fararen hula a yankin mai amfani da Turancin Ingilishi.
Matakin dai na tabbatar da zargin da ake yiwa dakarun sojin da aiwatar da kisan kiyashi kan fararen hula a yankin mai amfani da Turancin Ingilishi. REUTERS/Joe Penney
Talla

A cikin makon da ya gabata, babban hafsan sojin ya amince a wata zantawa da manema labarai cewa sojojin kasar sun kona gidaje da dama a yankin na ‘yan aware, ikirarin da ke tabbatar da zargin da aka jima ana yi wa jami’an tsaron kasar ta Kamaru.

Yankin na Kamaru mai amfani da Turancin Ingilishi dai na ci gaba da fukantar rikice-rikice baya ga karuwar ayyukan ta'addanci tun bayan rikicin da ya tilastawa mutane da dama barin muhallansu.

Al'ummar yankin dai na zargin gwamnati da nuna musu halin ko'in kula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.