Isa ga babban shafi
Najeriya

Yan sandan Najeriya sun gayyaci Bukola Saraki domin amsa tambayoyi

Rundunar yan sandan Najeriya ta gayyaci Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki domin amsa tambayoyi kan wasu yan fashi da makami da suka ce suna da alaka da shi.

Bukola Saraki Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya
Bukola Saraki Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya punch
Talla

Kakakin yan sandan Jimoh Moshood yace 5 daga cikin yan fashi 22 da aka kama sakamakon kazamin fashin da akayi a Offa wanda yayi sanadiyar kashe mutane 17 cikin su harda Yan Sanda 9, sun bayyana alakar su da shugaban Majalisar Dattawan.

Moshood yace wannan ya sa rundunar yan sandan ta gayyace shi domin yin bayani kan alakar sa da yan fashin.

Makwanni 3 da suka gabata, Sanata Bukola Saraki yayi zargin cewar Rundunar na shirin bata masa suna, bayan ta kwaso wasu yan fashi daga Jihar kwara zuwa Abuja, abinda ya sa Majalisar Dattawa ta tura wakilai domin ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.