Isa ga babban shafi

Kwamitin Sulhu ya kakabawa Sudan ta Kudu sabon takunkumi

Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya, ya kakabawa kasar Sudan ta Kudu takunkumin haramta mata sayan makamai.

Wasu mayakan sa kai daga kabilar Nuer a kasar Sudan ta Kudu, da ke jihar Upper Nile.
Wasu mayakan sa kai daga kabilar Nuer a kasar Sudan ta Kudu, da ke jihar Upper Nile. REUTERS/Goran Tomasevic
Talla

Kudurin da Amurka ta gabatar dai ya samu amincewar kwamitin ne bayan samun kuriu tara da ya ke bukata a zauren kwamitin tsaron, yayin da Rasha, China, Habasha, Bolivia, Equatorial Guinea da Kazakhstan suka ki amincewa da kudurin, bisa dalilan cewa, bangaren gwamnati da na ‘yan tawayen kasar kan kokarin cimma tabattaccen sulhun kawo karshen yakin kasar.

Amurka da wasu kasashen Turai sun jima suna kiran da a kakabawa sudan ta kudu takunkumin cinikin makamai, sai dai Amurka ta gaza samun nasara kan bukatar a watan Disambar 2016, da ta mika kudurin ga kwamitin tsaron na Majalisar dinkin duniyar.

A shekarar 2013, yakin basasa ya barke a Sudan ta Kudu shekaru 2 bayan samun 'yancin kai daga Sudan.

Rikicin ya soma ne bayan da shugaban Sudan ta Kudun Salva Kiir ya zargi mataimakinsa Riek Machar da yunkurin yi masa juyin mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.