Isa ga babban shafi
Jamhuri'yyar Demokradiyyar Congo

Jam'iyyun adawa sun nemi janyewar Kabila a zaben Congo

Hadakar Jam’iyyun adawa a Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo sun yi kira ga shugaba Joseph Kabila kan dole ya janye aniyarsa ta sake tsayawa takarar shugabanci a kasar da ke tafe a watan Disamba ko kuma su janye kudirin su na kauracewa zaben.

Hadakar Jam'iyyun wadan a baya suka yi barazanar kauracewa zaben, sanarwar ta ce baza su kauracewa zaben ba kuma baza su amince da takarar Kabila ba.
Hadakar Jam'iyyun wadan a baya suka yi barazanar kauracewa zaben, sanarwar ta ce baza su kauracewa zaben ba kuma baza su amince da takarar Kabila ba. © AFP
Talla

Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da jam’iyyun biyar suka fitar, wadda a ciki suka  zayyana bukatunsu gabanni babban zaben kasar na ranar 23 ga watan Disamba mai zuwa, sun ce matakin na Kabila ka iya rura wutar rikicin kasar.

Daga cikin bukatun da hadakar Jam'iyyun adawar suka zayyana a sanarwar sun ce basu amince da Kabila a matsayin dan takara ba, haka zalika basu amince da tsarin amfani da na'urar zabe da kasar ta bijiro da shi ba wanda sanarwar ta yi zargin cewa Kabila na kokarin haddasa rikici ne a tsarin amfani da Na'urar.

Hadakar Jam'iyyun wadan a baya suka yi barazanar kauracewa zaben, sanarwar ta ce baza su kauracewa zaben ba kuma baza su amince da takarar Kabila ba.

Cikin Jam'iyyun da suka rattaba hannu kan sanarwar akwai sanannu a fagen adawa da Jam'iiyar Kabila da suka kunshi ta UD da UDPS da kuma wadda Jean-Pierre Bemba ke jagoranta.

Kabila da ke kan kujerar shugabancin kasar mai arzikin ma’adinai tun a shekarar 2001, kasar da ta yi kaurin suna wajen cin hanci da rashawa, ta kuma fada rikicin kabilanci da na siyasa tun samun 'yancin kai, yanzu haka rikicin kasar ya lakume dubunan rayuka yayinda ake bayyana ta a matsayin kasa mafi take hakkin bil’adama a yammacin sahara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.