Isa ga babban shafi

Najeriya ta aike da karin soji dubu guda da jiragen yaki Zamfara

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bada umurnin tura karin dakarun soji dubu guda 1,000 domin aikin samar da tsaro a Zamfara ganin yadda Yan bindiga ke cigaba da cin Karen su babu babbaka a jihar Zamfara.

Ko a baya ma dai Gwamnatin Najeriyar ta aike da wasu jirage don yin shawagi a cikin dazukan da 'yan bindiga ke buya.
Ko a baya ma dai Gwamnatin Najeriyar ta aike da wasu jirage don yin shawagi a cikin dazukan da 'yan bindiga ke buya. FAYEZ NURELDINE/AFP
Talla

Matakin na shugaba Muhammadu Buhari na zuwa ne a dai dai lokacin da garuruwa fiye da 10 su ka yi hijira daga garuruwansu tare da shiga birane don tsira da rayukansu.

A bayan bayan nan dai hare-haren a Zamfara na ci gaba da tsananta dalili kenan da wasu ke ganin akwai bukatar karin jami'an tsaro, ko da dai wasu na ganin karin jami'an ba zai amfanar ba matukar ba a tura jami'an tsaron cikin dazuka da kauyukan da ake kai hare-haren ba.

Rahotanni na nuni da cewa galibin Jami'an tsaron na tarewa a birane ne maimakon shiga garuruwan da 'yan bindigar ke kai farmaki.

Ko a baya ma dai Gwamnatin Najeriyar ta aike da wasu jirage don yin shawagi a cikin dazukan da 'yan bindiga ke buya.

Haka zalika gwamnatin Najeriya ta amince da kafa wata bataliyar soji ta musamman a jihar Katsina don kawo karshen kashe-kashen da ake fuskanta a yankunan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.