Mutane 4 sun kara mutuwa sakamakon Ebola a Jamhuriyar Congo
Hukumomin Lafiya a Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo sun sanar da cewar an sake samun Karin mutane 4 da suka rasa rayukan su sakamakon kamuwa da cutar Ebola, makonni biyu bayan an sanar da magance cutar da ta hallaka mutane 33.
Wallafawa ranar:
Sanarwar ma’aikatar lafiyar ta ce mutanen 4 sun mutu ne a Beni da ke Arewacin Kivu, abinda ya kawo adadin wadanda suka mutu yanzu zuwa 7.
Alkaluman da hukumomi suka bayar sun nuna cewar, mutane 43 ne ake zargin sun kamu da cutar, yayinda aka tabbatar da 16 daga ciki, sai kuma 27 wadanda har yanzu ake da shakku kan su.
Yau Laraba ake saran hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya za ta fara aikin bayar da rigakafin cutar a yankin da aka samu barkewarta a kasar ta Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu