Isa ga babban shafi
Mali

MDD ta zargi jami'an tsaron Mali da yiwa fararen hula kisan gilla

Wani rahoton majalisar dinkin duniya ya zargi dakarun sojin Mali da tauye hakkin dan adam ta hanyar yiwa wasu fararen hula kisan gilla da sunan yaki da ‘yan ta’adda.

Wasu daga cikin sojin Mali da na Faransa yayin atasayen hadin gwiwa na yakar ta'addanci. 17 ga watan Okotoba, 2017.
Wasu daga cikin sojin Mali da na Faransa yayin atasayen hadin gwiwa na yakar ta'addanci. 17 ga watan Okotoba, 2017. REUTERS/Benoit Tessier/File Photo
Talla

Tuni dai gwamnatin ta Mali ta amsa cewa lallai akwai hannun wasu daga cikin jami’an tsaronta wajen tafka wannan ta’asa, bayan da aka gano wasu manyan kaburbura a yankin tsakiyar kasar, a tsakanin watannin Fabarairu da Yuli na wannan shekara.

Rahoton ya bayyana wasu lokuta da sojin Mali suka hallaka wadanda basu jib a basu gani ba, daga ciki, akwai samamen da suka kan wata kasuwar dabbobi, inda suka hallaka mutane 12 a watan Mayu.

A cewar rahoton na Majalisar dinkin duniya, a watan Yuni kuwa an gano wasu manyan kaburbura uku, dauke da gawarwakin mutane 25, wadanda bayan bincike aka gano cewa, fararen hula ne da jami’an tsaron kasar suka kama, a lokacin da suke gudanar da binciken gida-gida domin neman ‘yan ta’adda.

Majalisar dinkin duniyar ta koka bisa cewar har yanzu babu wani mataki da aka dauka kan sojin da ake zargi da aikata laifukan kisan gillar, duk kuwa da cewa gwamnatin Mali ta kaddamar da bincike kan zarge-zargen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.