Isa ga babban shafi
Najeriya-Buhari

Buhari ya koma Najeriya bayan kammala hutunsa a london

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma gida bayan gajeren hutu na kwanaki 10 da ya yi a birnin London na Birtaniya. Shugaban ya samu tarbe daga mukarraban gwamnati dama dubban masu goyon bayansa a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke babban birnin kasar Abuja.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. NAN
Talla

Tun a ranar 3 ga watan Agusta, 2018, shugaban ya fara hutun kwanaki 10 a birnin London inda mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo ya ci gaba da tafiyar da al’amuran kasar a matsayi mukaddashin shugaba.

Daga cikin muhimman ayyukan da mataimakin shugaban Najeriyar, Farfesa Yemi Osinbajo ya zartar akwai sauya shugabancin hukumar jami’an tsaron farin kaya ta DSS, inda ya maye gurbin Lawal Daura da Mista Matthew Seiyefa.

Korar Lawal Daura daga mukaminsa ya biyo bayan umarnin da ya baiwa jami’an hukumar ta DSS na datse kofar shiga majalisun Najeriya a farkon watan Agusta , lamarin da haifar da ce-ce-ku-ce a ciki da wajen kasar.

Farfesa Osinbajo, ya kuma bada umarnin sauya fasalin shugabanci da ayyukan rundunar ‘yan sandan kasar ta musamman mai yaki da fashi da makami da sauran manyan laifuka wato SARS.

Umarnin yi wa rundunar garambawul ya biyo bayan koken jama’a da ya yawaita, kan yadda jami’an ‘yan sandan da ke karkashin rundunar ta SARS ke cin zarafin mutane yayin gudanar da ayyukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.