Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya mayar da martani kan ficewar sanatocin APC

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana mutunta dokokin demokradiya da ‘yancin zabin ra’ayi da kuma shirinsa na aiki tare da dukkanin mambobin Majalisar Tarayyar Kasar ba tare da la’akari da jam’iyyunsu ba.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da shugabannin majalisar dattijai, Bukola Saraki da ta wakilai, Yakubu Dogara
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da shugabannin majalisar dattijai, Bukola Saraki da ta wakilai, Yakubu Dogara guardian.ng
Talla

A yayin mayar da martinin kan ficewar wasu Sanatoci da ‘yan Majalisun Dokoki daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar PDP mai adawa a ranar Talata, Buhari ya ce, babu daya daga cikinsu da ke da wata kullata a gare shi ko kuma gwamnatinsa.

Shugaban ya kara da cewa, shi ma bai kullaci ‘yan majalisun ba, kuma sauya shekarsu ba za ta yi illa ga damar da APC ke da ita ba ta sake lashe zabe mai zuwa.

Ko da dai shugaban ya ce, jam’iyyar APC ta yi iya bakin kokarinta don ganin ta dakile sauya shekar ‘yan majalisun, yayin da ya jinjina wa shugabancin jam’iyyar kan rawar da yake takawa wajen hada kan ‘yan’yanta.

Daga karshe shugaba Buhari ya yi fatan alheri ga daukacin wadanda suka koma jam'iyyar PDP daga APC.

Sanatoci 15 da wasu 'yan majalisun dokokin kasar suka fice daga APC a yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben shugaban kasa a shekara mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.