Isa ga babban shafi
Libya-'Yan cirani

Libya ta ki amincewa a dawo mata da bakin haure 177

Gwamnatin Libya ta yi watsi da yunkurin Italiya na mayar mata da bakin haure 177 wadanda suka samu tsallakawa kasar ta teku ba kuma tare da cimma yarjejeniya kan yadda za a rarraba su zuwa sauran kasashen Turai ba.

Libyan dai ita ke matsayin hanaya mafi sauki ga bakin hauren da ke son tsallakawa Turai don cirani, wanda kuma suka kara yawaita tun bayan hambarar da gwamnatin Mu'ammar Gaddafi a shekarar 2011.
Libyan dai ita ke matsayin hanaya mafi sauki ga bakin hauren da ke son tsallakawa Turai don cirani, wanda kuma suka kara yawaita tun bayan hambarar da gwamnatin Mu'ammar Gaddafi a shekarar 2011. Reuters
Talla

Ministan harkokin wajen Libya da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya Mohamed Siala, ya ce Libya baza ta amince da batun dawo da bakin hauren ba, domin kuwa yanzu haka ta na da akalla ‘yan cirani fiye da dari bakwai da ta ke kula da su.

A farkon makon nan ne, ministan cikin gida na Italy Matteo Salvini ya yi barazanar mayar da ‘yan ciranin su 177 Libya matukar tarayyar Turai ta gaza tattauna yadda za a lallabi Malta ta karbi wani kaso daga cikinsu tare kuma da tabbatar da bayar da kudaden kula da su.

Sai dai Mohamed Siala, ya ce Libya fa na matsayin hanyar wucewar bakin hauren ne kadai amma ba ‘yan kasar ba ne, maimakon haka acewarsa kamata ya yi a tsananta kir aga shugabannin kasashen da suka fito don su rika daukar matakan zuwa kwashe su.

Tun a ranar Litinin da ta gabata ne, jirgin ruwan Diciotti mallakin Italiya ya ceto ‘yan ciranin su 177 daga teku, yayin da su ke yashe a wani sansani da ke gab da tashar teku ta Sicilian a Catania ba tare da cimma matsaya kan yadda za a rarraba su ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.