Isa ga babban shafi
Italiya-Turai

Italiya ta yi barazanar mayar da 'Yancirani 180 Libya

Ministan cikin gida na Italiya Matteo Salvini ya fara barazanar mayar da ‘yan cirani kusan 180 da suka shafe kwanaki 3 a gabar ruwan kasar zuwa Libya matukar tarayyar Turai ta gaza tattauna da Malta kan yadda za a raba su.

Salvinin ya yi barazanar cewa ko dai Turai ta lalubo hanyar magance kwararowar 'yan ciranin daga Libya ko kuma ta fara mayar da su da zarar sun tsallako.
Salvinin ya yi barazanar cewa ko dai Turai ta lalubo hanyar magance kwararowar 'yan ciranin daga Libya ko kuma ta fara mayar da su da zarar sun tsallako. REUTERS/Guglielmo Mangiapane
Talla

Akalla ‘yan cirani 177 ne ke yashe a tsibirin Lampedusa da ke gabar ruwan Italiya tun ranar Alhamis bayan ceto su da wani jirgin agajin kasar ya yi amma kuma kawo yanzu Malta ta ki amincewa da karbar koda guda daga cikinsu.

Cikin wata sanarwa da ya fitar yau din nan Salvinin ya ce ko dai Turai ta lalubo hanyoyin kawo karshen safarar mutane tare da daura damarar raba 'yan ciranin da suka shigo Italiyan zuwa sauran kasashen Turai ko kuma ta iza keyarsu zuwa Libya.

Sanarwar ta Salvinin ta kuma bukaci hada kudaden da za a kula da 'yan ciranin kafin rarraba su ko kuma iza keyar ta su zuwa gida.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.