Isa ga babban shafi
China-Najeriya

China za ta ba Najeriya bashin dala miliyan 328 don bunkasa sadarwa

Fadar shugaban Najeriya ta ce China ta amince da bai wa Najeriya rancen dalar Amurka miliyan 328 don bunkasa harkokin sadarwa a kasar da ke yankin yammacin Afrika.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na China Xi Jinpin yayin ganawarsa a birnin Beijing gabanin fara taron kwanaki 6 na kasashen Afrika da China wanda ke da nufin bunkasa kasuwancin da ke tsakaninsu.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na China Xi Jinpin yayin ganawarsa a birnin Beijing gabanin fara taron kwanaki 6 na kasashen Afrika da China wanda ke da nufin bunkasa kasuwancin da ke tsakaninsu. Reuters
Talla

Sanarwar na zuwa ne kwana guda da fara ziyarar kwanaki 6 da shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya fara zuwa kasar ta China don halartar taron bunksa harkokin kasuwanci tsakanin Chinar da nahiyar Afrika.

Harkokin sadarwa na matsayin babban kalubale ga Najeriyar mai arzikin man fetur kuma sananniya da ke kan gaba a jerin kasashe mafiya karfin tattalin arziki na nahiyar ta Afrika.

Yarjejeniyar bayar da bashin na Dala miliyan 328 daga Chinar zuwa ga Najeriya ita ce yarjejeniyar baya-bayan nan da Buharin ke cimmawa da Beijing tun bayan hawansa karagar mulki a shekarar 2015 a dai dai lokacin da Chinar ke kokarin kara dankon alakar kasuwanci tsakaninta da Afrika.

Sanarwar ta Fadar shugaban Najeriya da ta wallafa a shafinta na Twitter ya nuna cewa yarjejeniyar za ta gudana ne tsakanin kamfanin Galaxy na Najeriya da kuma katafaren kamfanin sadarwar China Huawei.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.