Mutane da dama sun mutu a harin da Boko Haram ta kai Gundumbali
Ana fargabar mutane da dama sun rasa rayukansu bayan wani hari da mayakan boko haram suka kai kauyen Gundumbali da ke wajen birnin Maiduguri na jihar Borno a yankin arewa maso gabashin Najeriya yau Asabar.
Wallafawa ranar:
Rahotanni sun ce mayakan na Boko Haram sanye da kayan soji sun yiwa garin na Gudumbali tsinke yayinda suka fara harbi kan jami’an sojin da ke bayar da tsaro ga garin matakin da ya tilastawa sojin hade da fararen hula tserewa don tsira da rayukansu.
A watan Yunin daya gabata ne gwamnatin Najeriyar ta yi umarnin mayar da al’ummar garin na Gudunbula da ke yankin Guzamala matsugunansu la’akari da yadda ake samun nasara kan kungiyar ta Boko haram da ta addabi yankin.
Wani mazaunin garin da aka bayyana sunanshi da Muhammad ya ce kawo yanzu basu kayyade adadin mutanen da suka mutu a harin ba, ko da dai rundunar sojin ta Najeriya ta haramta musu magana da manema labarai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu