Isa ga babban shafi
Tanzania

Ana Ci Gaba Da Binne Gawan Mutane 224 Da Suka Yi Hadari A Tanzania

Rahotanni daga kasar Tanzania na cewa yau Littini an ci gaba da binne gawan mutane 224 da suka mutu sakamakon hadarin kwale-kwale da suke ciki a tafkin Victoria.Tun jiya lahadi aka binne gawa 12 a tsubirin Ukara inda kwale-kwalen zashi tun da fari.

Masu aikin ceto a tafkin  Victoria na kasar Tanzania
Masu aikin ceto a tafkin Victoria na kasar Tanzania Reuters TV/via REUTERS
Talla

Firaministan kasar Tanzania Kassim Majaliwa  ya jagoranci fara binne gawarwakin a jiya lahadi, inda ya nuna hadarin ya girgiza kasar baki daya, al'amarin daya sa ala tilas a ware zaman makoki a fadin kasar.

Sauran gawarwakin mutanen, dangi da ‘yan uwa suka karbin abinsu, don tafiya da su  binnewa da kansu, duk da cewa akasarin gawarwakin an gaza tantance mamatan.

A cewar Firaministan za’a gina wuri na musamman a Ukara, don tunawa da wadannan mamata, sannan kuma za’a kaddamar da hukumar binciken musabbabin wannan hadari.

Kasancewar tun alhamis aka sami hadarin, masu aikin ceto  sun fitar da tsammanin sake ganin wani da sauran numfashi

Sai dai kuma acewar Firaministan masu aikin ceto zasu ci gaba da laluben karkashin ruwa watakila a dace a sami wasu da ake ganin sun bace bayan hadarin.

Ministan Sufuri Isack Kamwelwa ya gaskata cewa kwale-kwalen na dauke da fasinjoji 265 ne, duk da cewa ya dace fasinjojin dake cikinsa bai kamata su zarce 100 ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.