Isa ga babban shafi
Wasanni

Kenya ta fita daga zargin goyon bayan shan kwayoyin karin kuzari

Hukumar sa ido kan wasannin motsa jiki, mai yaki da shan kwayoyin karin kuzari ta duniya WADA, ta ce babu wata hujja da ke nuna gwamnatin Kenya na goyon bayan ‘yan wasanta kan haramtacciyar dabi’ar shan kwayoyin karin kuzari ba bisa ka’ida ba.

Data daga cikin 'yan wasan da suka wakilci Kenya a gasar Olympics ta 2016 da Brazil ta karbi bakunci, David Lekuta Rudisha.
Data daga cikin 'yan wasan da suka wakilci Kenya a gasar Olympics ta 2016 da Brazil ta karbi bakunci, David Lekuta Rudisha. REUTERS/Dylan Martinez
Talla

A watan Disamba na shekarar 2016 WADA ta kaddamar da bincike kan zargin cewa gwamnatin Kenya na marawa masu wasannin motsa jikin kasar wajen shan kwayoyin karin kuzari, musamman a bangaren masu wakiltarta a gasar tseren gudun yada kanin wani.

Duk da cewa hukumar WADA bata samu gwamnatin Kenya da laifi ba, bincikenta na shekaru 2, ya bankado ‘yan wasan motsa jikin kasar 138 da suka yi amfani da kayoyin karin kuzari.

Binciken ya gano cewa 113 daga cikin 'yan wasan da aka samu da laifin, sun yi amfani da haramtattun kwayoyin ne, a wasannin da suka fafata daga shekarar 2004 zuwa ranar 1 ga watan Agusta na shekarar 2018.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.