Isa ga babban shafi
Kenya

Mutane 51 sun mutu a hadarin mota a Kenya

Mahukuntan Kenya sun tabbatar da mutuwar mutane akalla 51, yayin da wasu da dama suka jikkata, bayan da wata motar Safa da suke ciki ta kife a yankin yammacin kasar.

Motar da ta yi hatsari a Kenya
Motar da ta yi hatsari a Kenya ewn.co.za
Talla

A cewar babban jami’in ‘yan sandan yankin Kericho, in da hadarin ya auku, James Mogera, adadin wadanda suka rasa rayukansu na iya karuwa, yayin da ya dora alhakin hadarin kan rashin bin ka’idojin tuki.

Rahotanni sun ce, mutane akalla goma aka garzaya da su asibiti, sakakamakon raunin da suka samu a hadarin da kananan yara ‘yan kasa da shekaru biyar suka hallaka.

Wani wanda ya tsira da ransa a hadarin y ace,

“A lokacin da muke cikin Bus din, muna ta tadi tsakaninmu fasinjoji, har muna cewa ko da zamu isa da karfe 10 na safe, zai mana dai-dai.

Tun tasowarmu daga Nairobi, komai na tafiya dai-dai a motar, birikinta na aiki, to amma da muka wuce Naivasha, lamari ya fara sauyawa, har motar ta kauce hanya kuma hadarin ya auku.”

Tuni shugaban kasar Uhuru Kenyatta ya aike da sakon ta’aziya ta shafinsa na Twitter.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.