Isa ga babban shafi
Sudan

Zanga-zanga kan farashin biredi ta kazanta a Sudan

Rahotanni daga Sudan sun ce mutane 22 sun rasa rayukansu, yayin da dubban mutane suka ci gaba da zanga-zangar adawa da matakin gwamnati na kara farashin Biredi da kuma sauran matsalolin tattalin arziki da suke fuskanta.

Masu zanga-zanga sun yi arrangama da jami'an tsaro a Sudan kan farashin biredi.
Masu zanga-zanga sun yi arrangama da jami'an tsaro a Sudan kan farashin biredi. Reuters/Thierry Roge
Talla

Tun a ranar Laraba zanga-zangar ta soma bayan da gwamnati ta sanar da karin farashin biredin daga kudin kasar fan daya zuwa uku.

Zanga-zangar da aka soma a garin Atbara ta bazu zuwa Gadarif da ke gabashin kasar, kafin isa babban birnin kasar Khartoum, Omdurman da wasu sassan kasar.

Tuni dai gwamnati ta kafa dokar ta baci a birnin Gadarif inda masu zanga-zanga akalla 6 suka mutu yayin arrangama da jami’an tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.