Isa ga babban shafi
Sudan

Mutane 24 sun mutu a zanga-zangar Sudan

Kwamitin da Sudan ta kafa don sa ido kan boren da wasu ‘yan kasar ke yi, ya ce mutane 24 sun mutu bayan soma zanga-zangar daga Disamba zuwa yanzu.

Wasu masu zanga-zanga a Sudan.
Wasu masu zanga-zanga a Sudan. REUTERS/Mohamed Nureldin Abdallah
Talla

Sai dai kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch ta ce yawan wadanda suka rasa rayukansu ya kai akalla 40, a dalilin arrangamar masu zanga-zangar da jami’an tsaro a lokuta daban daban.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun zargi ‘yan sandan Sudan da yin amfani da harsashi mai kisa, da hayaki mai sa hawaye kan masu zanga-zanga, matakin da suka ce ya taka rawa wajen yawaitar wadanda suka hallaka.

Tun a ranar 19 ga Disamba zanga-zanga ta soma kan adawa da karin farashin Biredi, wadda ta juye zuwa ta neman saukar shugaba Omar Hassan al-Bashir daga shugabancin kasar.

Shugaba al-Bashir da kotun duniya ta ICC ke nema ‘ruwa a jallo’ ya dora alhakin tashe tashen hankulan kan wasu makiyan Sudan a ciki da wajen kasar, inda kuma ya zargi Amurka da jefa kasar cikin kangin wahala, bayan kakaba mata takunkumin karya tattalin arziki a shekarar 1997 zuwa 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.