Isa ga babban shafi
Sudan

Shugaba al-Bashir ya kafa dokar ta baci a Sudan

Jagororin dubban jama’ar da ke kin jinin gwamnatin Sudan, sun sha alwashin ci ga da zanga-zanga,har sai sun cimma burin tilastawa shugaban kasar Omar Hassan al-Bashir yin Murabus.

Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir.
Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir. AFP/ASHRAF SHAZLY
Talla

Shugabannin zanga-zangar sun sha alwashin ne jimkadan bayanda shugaba al-Bashir ya bayyana kafa dokar ta baci a ilahirin kasarta Sudan, wadda za ta shafe tsawon shekara guda tana aiki.

Yayin sanar da kafa dokar ta bacin shugaba al-Bashir ya bayyana rushe gwamnatin kasar daga matakin tarayya zuwa na lardunan, domin kawo karshen zanga-zangar da ‘yan kasar suka shafe sama da watanni 2 suna yi ta neman tilasta masa ya sauka daga mulki, bayan shafe sama da shekaru 29 yana jagorantarsu.

A ranar 19 ga watan Disambar 2018, zanga-zanga ta barke a wasu manyan biranen Sudan, domin nuna adawa da Karin farashin biredi.

Daga bisani zanga-zangar ta juye zuwa ta kin jinin gwamnati, bisa zarginta da gazawa wajen maganace matsalar tattalin arzikin da ke damun ‘yan kasar, wadda kuma ta bazu zuwa sauran biranen kasar.

Alkalumman da gwamnati ta fitar sun nuna cewa mutane 31 suka mutu yayin zanga-zangar ta sama da watanni 2, a lokacin da suka rika arrangama da jami’an tsaro, sai dai kungiyoyin kare hakkin dan adam sun ce adadin mamatan ya kai akalla 51.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.