Isa ga babban shafi
Mali

Gwamnatin Mali ta kori manyan jami'an sojinta

Gwamnatin Mali ta kori wasu manyan jami’an sojinta, sakamakon farmakin da aka kai kan kauyen Ogassogou da ke yankin tsakiyar kasar inda aka hallaka Fulani 134.

Wasu dakarun sojin kasar Mali.
Wasu dakarun sojin kasar Mali. AFP/Philippe Desmazes
Talla

Gwamnatin ta Mali ta kuma rushe kungiyar Ambassagou da mafarautan kabilar Dogon, wadanda ake zargi da kai kazamin harin na baya bayan nan.

Koda yake ba’a bayyana sunayen jami’an sojin da aka kora ba, Fira Ministan Mali Soume’ilu Boubaye Maiga, yace za’a bayyana sunayen sabbin manyan jami’an nan da gajeren lokaci.

Tuni dai Sakataren Majalisar ta Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci gaggauta bincike da hukunta wadanda suka tafka ta’asar.

Wata majiyar tsaron kasar ta Mali tace gawarwakin Fulanin na dauke ne da ranukuna harbi da bindiga ko sara da wuka.

Wadanda suka tsira sun zargi mafarautan kabilar Dogon da kai mumunan harin, kabilar da aka zarga da hallaka Fulani 37 a kauyen Koulogon da ke yankin tsakiyar kasar ta Mali cikin watan Janairu.

Rikici kan filaye da ruwan sha tsakanin kabilun da ke zaune a yankin tsakiyar Mali ne ya girmama zuwa fadan kabilanci, musamman tsakanin Fulani da kabilar Dogon, tashin hankalin da yayi sanadin salwantar rayuka 500 a shekarar bara, a cewar Majalisar dinkin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.