Isa ga babban shafi
Afrika

Najeriya da Ghana na ganawa kan matsalolin shige da fice

Shugaban rundunar shige da fice na Ghana Kwame Takyi ya samu ganawa da Shugaban jami’an shige da fice na Najeriya Mohammed Babadede a ofishin sa dake Abuja don duba hanyoyin da ya dace kasashen biyu su bi don warware tsaikon da ake fuskanta mako daya bayan da Hukumomin Najeriya suka mayar da wasu yan Ghana hudu kasar su ta asali.

Wasu daga cikin yan kasar Ghana dake fatan gani an kawo karshen wannan matsalla
Wasu daga cikin yan kasar Ghana dake fatan gani an kawo karshen wannan matsalla RFI / Pierre René-Worms
Talla

Indan aka yi tuni wata daya da suka gabata hukumomin Najeriya sun bayyana damuwa bayan da hukumomin Ghana suka kori wasu yan Najeriya 723 kama daga shekara ta 2018 zuwa watan Fabrairu shekarar 2019.

Hukumomin Ghana sun bayyana damuwa matuka ,kasancewar kasashen biyu na cikin kungiyar Ecowas,a hakan suka kuma kasa cimma matsaya a baya,sabili da haka Ghana ta aiko da Shugaban shige da fice zuwa Najeriya.

Ana dai zargin yan Najeriya da zama cikin kasar Ghana ba tareda sun malaki takardun zama ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.